✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufa’i zai daure iyayen yaran da ke bara

Gwamnatin jihar Kaduna ya ta ce duk iyayen da aka samu ‘ya’yansu na bara a jihar to za su fuskanci hukunci da  daurin shekara biyu.…

Gwamnatin jihar Kaduna ya ta ce duk iyayen da aka samu ‘ya’yansu na bara a jihar to za su fuskanci hukunci da  daurin shekara biyu.

Kazalika duk malamin da aka samu ya dauki almajirai a jihar, to za a ci shi tarar Naira 100,000 zuwa 200,000 a kan kowane yaro.

Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana hakan yayin ziyarar almajirai 200 ‘yan asalin jihar da aka dawo da su daga jihar Nasarawa.

Da yake magana a cibiyar kula da tantance lafiyar almajiran da ke makarantar Government College, Kurmin Mashi, El-Rufa’i ya ce yaba da yadda ake aikin sauya tunanin yaran domin inganta rayuwarsu.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ba wa yaran damar cimma burace-burancesu a matsayinsu na ‘yan jihar Kaduna.

“Za mu sa su a makarantun boko a unguwannin da iyayensu ke zama.

“Za mu dage da yin haka har sai mun yaki almajiranci wanda wani salo ne na tauye hakki da kuma dankwafe rayuwar yara.

“Manufarmu ita ce ba wa yaran ilimin boko ba tare da hana su karatun Alkura’ni ba. Za su ci gaba da karatun Alkur’ani amma a gaban iyayensu ba wani wanda ake biya ya kula da su ba.

El-Rufaiya ce Ma’aikatar Kula da Ci Gaban Jama’a ta jihar (MHSSD) za ta yi aiki tare da Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) domin tabbatar da babu yaron da zai ba cibiyar ba tare da ya kammala karatun firamare da karamar sakandare ba.

“Daga nan wadanda ba za su iya ci gaba da karatu ba za a ba su damar koyan sana’o’i kyauta.

“Don haka iyaye ba su da wata hujja na kin tura ‘ya’yansu makaranta,” inji shi.