Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci dukkan makarantun gwamnati a Jihar da su koma aiki kwana hudu a mako daga ranar 10 ga watan Janairun 2022.
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar, Halima Lawal, ce ta ba da umarnin a Kaduna ranar Lahadi a wata wasika da ta aike wa makarantun a zangon karatu na 2021-2022.
- Fasinjoji sun yi curko-curko bayan direbobin Adaidaita Sahu sun tsunduma yajin aiki a Kano
- Babu maganar sulhu tsakanina da Ganduje — Kwankwaso
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a ranar daya ga watan Disamban bara ne gwamnatin ta fara aiki da sabuwar dokar ta aikin kwanaki hudu a mako.
A cikin wata sanarwa da mai ba Gwamnan shawara a kan yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar, ya ce sannu a hankali matakin zai shafi hatta kamfanoni masu zaman kansu a Jihar.
Gwamnatin dai ta ce matakin zai taimaka wa ma’aikatanta su kara kwazo sannan su samu lokacin iyalansu da na hutu da kuma na yin noma.
A cewar Kwamishiniyar, matakin zai sa a canza tsarin koyo da koyarwa a zangon karatun na bana.
Ta ce iyayen yara su lura cewa gwamnatin ta amince da ranar Litinin, 10 ga watan Janairun 2022 a matsayin ranar da za a dawo domin fara zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2021/2022.
“Ma’aikatar Ilimi na son dukkan shugabannin makarantun sakandire da Firamare su fara karbar daliban kwana daga ranar tara ga watan Janairun 2022.
“Bugu da kari, ma’aikatar na shawartar iyaye da dalibai su bi dukkan matakan kariyar COVID-19.
“Shugabannin makarantu masu zaman kansu da na Islamiyya su ma ana bukatarsu su da su ci gaba da kiyaye matakan tsaro a makarantunsu,” inji ta. (NAN)