✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya tasa keyar Almajirai 35,000 daga Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta mayar da kananan Almajirai 35,000 zuwa jihohi 17 da wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya. Kwamishiniyar Jin-kai da Inganta Rayuwar…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta mayar da kananan Almajirai 35,000 zuwa jihohi 17 da wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Kwamishiniyar Jin-kai da Inganta Rayuwar Al’umma ta Jihar, Hajiya Hafsat Baba ta bayyana hakan a hirarta da kamfanin dillacin labarai (NAN) a Kaduna.

Da take jawabi, Hafsat Baba ta ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da kudirinta na ganin cewar kowane yaro ya samu ilimin addini da na zamani karkashin kulawar iyayensa.

Kwamishiniyar ta ce, kawo yanzu Jihar Kaduna ta karbi sama da Almajirai 1,000 daga jihohi daban-daban na kasar nan.

Ta ce, Hukumar Tallafa wa Ilimin Kanan Yara (UNICEF), ta taimaka wa ma’aikatarta wajen tattara bayanai da bayar da shawarwari da kuma magance rashin lafiyar Almajiran da jihar Kaduna ta karba daga wasu jahohin.

Hakan yana da matukar muhimmanci domin bayan cutar COVID-19, wasu daga cikin Almajiran na dauke da wasu nau’ukan cututtuka da ke bukatar kulawa kafin a mika su ga iyayensu.

Hafsat ta kara da cewar ma’aikatarta na sane da cewar hakkin gwamnati ne ta ilmantar da yara wanda shi ya sa suke kokarin bijiro da makarantun Tsangaya a fadin Jihar.

“A nan muna so mu yi la’akari da kusanci da dacewar inda ya kamata a sanya Almajiran makarantar sa za su koyi ilmin addini da boko ba tare da sun yi tafiya mai nisa ba.”

Ta kara da cewar Gwamnatin Jihar shirye take ta karbi duk wani Almajirinta da aka kawo daga wata jiha, kuma za ta ci gaba da daukar malaman addini, da kuma fahimtar da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma cewar dole ne iyayen yaran su kula da rayuwarsu.