✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Kudancin Kaduna

Dokar hana fitar ta fara aiki nan take a kananan hukumomin Kaura da Jema'a

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita na sa’a 24 nan take a kananan hukumomin Kaura da Jema’a da ke Jihar

A safiyar Litinin Kwamishin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar da kafa dokar ta hana fita bisa shawarar hukumomin tsaro, sakamakon hatsaniya da karya doka da oda da aka samu yankin.

“Gwamnati na kira da daukacin al’ummar kananan hukumomin Jema’a da Kaura da su ba wa jami’an tsaro cikakken hadin kai domin dawo da doka da oda.

“Gwamanti ta yi Allah wadai da kowane nau’in rikici da karya doka da oda da aka samu a yankin,” inji Aruwan.

A cewarsa, an ba wa jami’an tsaro cikakken ikon tabbatar da bin dokar ta hana fita kuma matakin zai taimaka wajen daidaita al’amura da kuma dawo da doka da oda tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An rufe makarantu

Tun da fakro hare-haren da aka kai a yankin Agban da ke Marabar Kagoro zuwa hanyar Gidan Waya da ke kan iyakokin kananan hukumomin Kaura da Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna, sun sa an rufe makarantu da kasuwanni inda mazauna ke ta komawa zuwa inda mutanensu suka fi yawa.

Hakan, ba ya rasa nasaba da kisan wani dan garin Kafanchan mai suna Dan’asabe da aka yi da safiyar Litinin a kan hanyarsa ta shigowa Kafanchan daga Mariri, inda aka tare shi a Maraban Kagoro da ke hanyar shigowa garin Kafanchan aka kashe shi.

Kafin nan, ranar Lahadi da misalin karfe 9 na dare wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a yankin Kagoro da ke karamar hukumar Kaura.

Kawo yanzu dai motocin jami’an tsaro ne ke ta karakaina a manyan titunan Kafanchan.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige don jin karin bayani bai amsa wayar wakilinmu ba.