Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita na tsawon sa’a 24 sakamakon rikicin da ke neman kunno kai a masarautun jihar Guda biyu.
Dohar hana fitan ta fara aiki nan take ta kuma shafi Masarautar Atyap a Karamar Hukumar Zangon Kataf da kuma Masarautar Chawai da ke Karamar Hukumar Kauru.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Samuel Aruwan ya ce rikicin ya samo asali ne daga rikicin gona a Zangon Kataf tun makon jiya.
Samuel Aruwan ya ce sarakuna na kokarin shawo kan matsalar wadda ta ki ci ta ki cinyewa.
Rahotanni sun nuna al’ummar Hausa-Fulani da makwabtansu Atyap a Zagon Kataf sun kusa ba wa hamata iska sakamakon rikicin filayen gonakin da kowane bangare ke ikirarin mallaka.
Tsintar gawar wani mutum da aka yi wa yankan rago da safiyar Alhamis a gefen rafi kan iyakar Zangon Kataf da Kauru ya haddasa cacar baki tsakanin bangarorin biyu.