✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya rattaba hannu a kasafin N376.4bn

Kasafin na 2023 ya bai wa fannin kiwon lafiya da na ilimi fifiko.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya rattaba hannu kan  dokar kasafin 2023 na sama da Naira biliyan N376.4.

Kwamishinar Kasafi da Tsare-tsare ta jihar, Umma Aboki, ta ce kasafin ya bai wa fannonin kiwon lafiya da ilimi muhimmanci inda suka samu kashi 43.70 cikin 100.

Ta bayyana wa manema labarai ranar Alhamis a Kaduna cewa, an ware wa manyan ayyuka biliyan N240.9, sai biliyan N135.5 domin ayyukan yau da kullum.

Umma ta ce, jihar na sa ran samun  biliyan N89.2 a matsayin kudin shiga na cikin gida, sannan biliyan N59.9 daga asusun tarayya badi idan Allah Ya kai mu.

Kazalika, jihar tatna sa ran samun harajin VAT na biliyan N30.7 da kuma bashin N62.7bn da N61.6bn da N20.9bn daga gida da waje.

Ta ce, duka wadannan kokarin da gwamnatin jihar ke yi ne domin cimma manufofinta na bunkasa jihar da kyuatta rayuwar al’umarta.

(NAN)