✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya bai wa Sanusi II babban mukami a jami’ar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya bai wa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukamin Uban Jami’ar jihar Kaduna (KASU). Wannan shi ne karo na…

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya bai wa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukamin Uban Jami’ar jihar Kaduna (KASU).

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan na jihar ta Kaduna ke bai wa tsohon sarkin mukami biyo bayan tube shi da aka yi daga gadon sarautar Kano

A wata takardar da mai taimakawa gwamnan akan harkokin sadarwa Mista Muyiwa Adekeye, ya rattabawa hannu na cewa, tubabben sarkin ya amince da mukamin da aka ba shi.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin jihar Kaduna ta nada Mai martaba Muhammadu Sanusi II a matsayin Uban jami’ar jihar Kaduna (KASU). Ya maye gurbin shugaban na farko, Mai martaba, Malam Tagwai Sambo wanda aka nada a shekarar 2005.”

Sanarwar ta kara da cewa, gwamna El-Rufai ya yi fatan sabon shugaban jami’ar zai bada gudunmawarsa da kuma jagoranci na gari wajen karfafa kimar jami’ar a matsayin cibiya mai ingataccen tsarin koyarwa.

El-Rufai ya bai wa Sarki Sanusi II mukami