Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba wa kananan ma’aikatanta kyautar albashin wata daya kowannensu, a matsayin kyuatar karshen shekara.
Gwamnan Nasir El-Rufai ne ya sanar da kyautar, a matsayin tukwici ga irin sadaukar da kan da ma’aikatan suke yi, da kuma kara musu kwarin gwiwa.
- Mawaki Umar M. Shareef ya zama jakadan gidan talabijin na Qausain
- Fitattun fina-finan Kannywood da suka fi daukar hankali a bana
Sanarwar da kakakin gwamnan, Muyiwa Adekeye, ya fitar ta ce ta ce kyautar ta shafi dukkan ma’aikatan jihar, kuma gwamnatin ta ware Naira biliyan 1.3 domin wannan karimci.
Ya bayyana cewa ma’aikatan da ke matakin albashi na bakwai zuwa kasa za su samu kyautar albashinsu na wata guda-guda.
Daga mataki na takwas zuwa 13 kuma kyautar kashi 40 cikin 100, sai mataki na 14 zuwa sama da za a ba su kyautar kashi 30 cikin 100 na albashinsu.
A baya-bayan nan ne dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta rage yawan ranakun zuwa aikin ma’aikatanta zuwa kwana hudu a mako.