Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ba da umarnin bude masallatan Juma’a da coci-coci domin a ci gaba da gudanar da ibadu bayan rufe su na tsawon watanni biyu.
An rufe wuraren ibadan ne sama da kwanaki 75 da suka wuce a yunkurin jihar na dakile yaduwar cutar coronavirus.
Gwamna El’rufai ya bayyana dage dokar ne a jawabinsa ga jama’ar jihar a ranar Talata.
Ya ce daga yanzu jama’a za su rika fita daga 9:00 na safiya zuwa 3:00 na rana kullum daga ranar Laraba 10 ga watan Yunin 2020.
Makarantu da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci, saboda har yanzu akwai hadarin kamuwa da cutar.
- Dokar Kulle: El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin Kaduna
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
- Yadda na sha fama a killace har kwana 26 –El-Rufai
El-Rufai ya ce gwamnati na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar domin fito da hanyoyi da suka dace da za a dage dokar baki daya.
“Wuraren kasuwanci na iya bude su bisa sharadin za su rika amfani fa na’urar auna zafin jiki da wanke hannu da kuma da ba da tazara a tsakanin al’umma a lokutan fita daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana a kullum,” inji shi.
Ya ce “Za’a bude coci-coci ne ranakun Lahadi, masallatan Juma’a kuma a ranar Juma’a, muddin an kiyaye ka’idojin”.
Gwamnati za ta iya sake rufe wuraren matukar aka ki bin ka’idojin”, a cewar gwamnan.
Ya kara da cewa dole masu shekararu fiye 50 da haihuwa su rika taka-tsantsan saboda kauce wa kamuwa da cutar.
Sannan jamj’an tsaro za su ci gaba da ganin an bi dokar sanya takunkumi a fadin jihar.