Kungiyar Kwadago ta Nariya (NLC) ta ce za ta koma yajin aikin da ta dakatar muddin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ki zama a daidaita kan sallamar ma’aikatan da ya yi.
NLC ta ce kofarta a bude yake domin tattauwa tare da magance matsalar da Gwamnatin Jihar Kaduna, amma idan El-Rufai ya ki yarda a nemo mafita mai dorewa, to ’yan kwadago a fadin Najeriya za su tsunduma yajin aiki.
“Idan Gwamnatin Jihar Kaduna ta ci gaba da cijewa ko yakar ma’aikata ko yi musu kutungwila, an ba Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NAC) iko nan take ya ci gaba da yajin aikin da aka dakatar a Jihar Kaduna, ya kuma kira a fadin Najeriya ba tare da wata sabuwar sanarwa ba,” inji kungiyar bayan taron Kwamitin Zartarwarta na Kasa (NEC) ranar Alhamis.
Sanarwar da Shugaban NLC Ayuba Wabba da Mukaddashin Sakatarenta Ismail Bello suka sanya wa hannu ta ce, “NEC ta amince a bar kofar tattaunawa a bude domin kawo karshen matsalar da rashin tunani da haramtaccen matakin sallamar ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ya haifar.
El-Rufai da ’yan kwadagon sun sa zare a makon da ya gabata bayan gwamnan ya sallami ma’aikata 4,000 wanda NLC ta ce ya haramta, ta kuma shiga yajin aiki da zanga-zangar lumana.
Matakin kungiyar ya gurgunta harkoki na kwanaki a Jihar Kaduna, kafin Gwamnatin Tarayya ta sanya baki kungiyar ta janye yajin aikin a hau teburin sulhu.