Hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Dan Fadio, Sakkwato (UDUTH), ta nada Alhaji Abbati Dano El-Hamzat sabon Daraktan Gudanarwar asibitin.
Shugaban Hulda da Jama’a a UDUTH, Buhari Abubakar Sokoto ya sanar da cewa nadin ya fara aiki ne daga ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2020.
- An karrama direban Sardauna a bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa
- Maniyyata Umrah za su fara isa Saudiyya ranar Lahadi
Kafin samun wannan mukamin, El-Hamzat shi ne Babban Mataimakin Darakta (Mai kula da al’amuran Ma’aikata kuma Mukaddashin Daraktan Gudanarwan asibitin ).
El-Hamzat ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero, Kano, digirinsa na biyu kuma a bangaren Al’amuran Gudanarwar a Jami’ar Usmanu Dan Fadio da ke sakwkato.
Ya samu shaidar zama mamba a Gidauniyar Kula da Harkokin Lafiya ta Najeriya (IHSAN).