✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Clasico:  Jibi za a kece-raini a tsakanin Real Madrid da FC Barcelona

A jibi Lahadi ce ake sa ran za a kece-raini a wasan kwallon kafa mafi daukar hankalin duniya da aka fi sani da El-Clasico da…

A jibi Lahadi ce ake sa ran za a kece-raini a wasan kwallon kafa mafi daukar hankalin duniya da aka fi sani da El-Clasico da ake yi a gasar La-Liga ta Spain inda kulob din Real Madrid zai karbi bakuncin FC Barcelona.  Masana Wannan wasa shi ne mafi zafi a fadin duniya inda aka kiyasta kimanin mutum miliyan 500 ne suke kallon yadda wasan ke gudana a fadin duniya.

Kamar yadda jadawalin wasan ya nuna, wasan zai gudana ne a filin wasa na Santiago Bernebeu wato gidan Real Madrid da misalin karfe 9:00 na dare agogon Najeriya.

Za a gwabza wasan ne a tsakanin kungiyoyi biyu da suke saman teburin gasar La Liga a bana kawo yanzu wato FC Barcelona da kuma mai biye da ita Real Madrid. Idan Real Madrid ta samu nasara a wasan za ta haye teburin gasar da tazarar maki daya yayin da idan FC Barcelona ta samu nasara za ta ba Madrid tazarar maki biyar ke nan.

 

Tarihin Gasar:

Bayanai sun nuna cewa wannan shi ne karo na 276 da kungiyoyin biyu za su fafata a tsakaninsu  a wannan wasa.   Sai dai wasannin sun kunshi haduwar da suka yi a wasanni daban-daban da suka hada da na Zakarun Turai (Champions League) da na Copa del Rey da La-Liga da sauransu.  Daga cikin wannan adadi, kulob din FC Barcelona ya samu nasara a wasa 115 yayin da Real Madrid kuma ya samu nasara a wasa  99 sannan suka yi kunnen doki sau 62.

 

Gasar La-Liga: 

A gasar La-Liga ta Spain tarihi ya nuna kungiyoyin biyu sun hadu sau 179 kawo yanzu inda dukkan kungiyoyin suka samu nasara a wasa 72 sannan suka yi kunnen doki sau 35. Ke nan za a iya cewa wasan jibi ne zai iya raba-gardama inda za a samu wadda za ta fi daya samun nasara a kan daya a tsakaninsu.  Amma idan suka tashi kunnen doki za su ci gaba da zama a haka sai kuma nan gaba.

 

’Yan kwallon da suka fi yawan buga wannan wasa:

Tarihi ya nuna ’yan kwallo uku ne suka fi yawan buga wannan wasa da suka hada da ’yan kwallon Real Madrid Sergio Ramos da Manolo Sanchis wanda ya yi wa Real Madrid wasa a tsakanin 1965 zuwa 1971 da kuma Francisco Gento. Dukkansu sun buga wannan wasa sau 42, sai dai Ramos zai kafa sabon tarihi idan ya yi wasan jibi inda zai kasance dan kwallon da ya fi kowa yawan buga wannan wasa don zai hada wasa 43 ke nan.  A bangaren Barcelona kuwa tsohon dan kwallonsu Dabi ne ya fi yin wannan wasa inda ya buga har sau 42.

 

’Yan kwallon da suka fi yawan zura kwallo a wasan:

Kawo yanzu Lionel Messi dan kwallon FC Barcelona ne ya fi yawan zura kwallaye a wannan wasa na El-Clasico inda yake da kwallo 26 sai tsofaffin ’yan kwallon Madrid Alfredo Di Stefano da Cristiasno Ronaldo da kowannensu yake da kwallo 18.

 

Wasan da aka fi yawan zura kwallaye:

Kulob din da ya fi yawan zura kwallaye a wa dan uwansa a tsakanin kungiyoyin biyu  shi ne wasan karshe a Kofin Copa del Rey da Real Madrid ta lallasa FC Barcelona da ci 11-1 a ranar 19 ga watan Yunin 1943.  Sai dai a baya-bayan nan Barcelona ta lallasa Madrid da ci 5-0 ,

 

Haduwarsu ta karshe:

Haduwar da kulob din biyu suka yi ta karshe ita ce ta ranar 18 ga watan Disamban bara a gasar La-Liga inda aka tashi kunnen doki 1-1 a filin wasa na Camp Nou na FC Barcelona.