✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El clasico: Gobe za a yi gumurzu tsakanin Barcelona da Real Madrid

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mafi zafi a tarihin kwallon kafa na duniya inda kungiyar kwallon kafa ta FC…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi wasa mafi zafi a tarihin kwallon kafa na duniya inda kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona za ta karbi bakuncin kulob din Real Madrid a gasar La-Liga ta Sifen.
An tabbatar a duk fadin duniya, babu wasan da ya kai wannan zafi a matakin na kulob-kulob inda aka kiyasta kimanin ’yan kallo miliyan 500 ne suke kallon yadda wasan ke kayawa a duk fadin duniya.   Hatta a gidajen kallon kwallo da ke Najeriya suna shaidawa ganin yadda suke samun kudin shiga a duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na Camp Nou na FC Barcelona da misalin karfe 4 da mini 15 agogon Najeriya.
Idan za a tuna a bara, kulob din FC Barcelona ne ya fara kai ziyara gidan Madrid kuma ya lallasa Madrid da ci 4-0 sai dai a wasa zagaye na biyu kulob din Madrid shi ma ya bi  Barcelona har gida ne inda ya lallasa ta da ci 2-1.
Kawo yanzu Madrid ce take samun teburin gasar da maki 33 a wasanni 13 yayin da Barcelona take biye da maki 27 a wasanni 13.
A tarihin haduwar kungiyoyin biyu a gasar ta La-Liga, sun hadu ne sau 170 inda Real Madrid ta samu nasara sau 70 yayin da FC Barcelona ta samu nasara sau 67.
Idan Barcelona ta samu nasara a wasan, ko shakka babu za ta rage tazarar makin da Madrid ta ba ta kuma za ta farfado da damar neman sake lashe gasar a bana.  Amma idan Real Madrid ta samu nasara a wasan to za ta sake yi wa Barcelona nisa a tazarar maki kuma hakan zai karfafa mata gwiwar cigaba da jan ragamar gasar.   Sannan kawo yanzu, Real Madrid ba ta samu rashin nasara a gasar ba tun bayan da aka fara kakar wasa ta bana da hakan ya nuna kungiyar na tashe yayin da FC Barcelona kuma ta samu rashin nasara har sau biyu.
Barcelona dai tana ji da zaratan ’yan kwallon gaba ne irin su Lionel Messi da Luis Suarez da kuma Neymar yayin da Real Madrid take tinkaho da zaratan ’yan kwallo irin su Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Gareth Bale da sauransu.
Sai dai masu iya magana sun ce ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare, don haka duniya ta zuba ido ta ga yadda wasan zai kaya a goben.