✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Clasico:  Gobe Madrid za ta sake karawa da FC Barcelona

A gobe Asabar ake sa ran kulob din Real Madrid zai sake karawa da na FC Barcelona kwana uku kacal bayan sun hadu a gasar cin…

A gobe Asabar ake sa ran kulob din Real Madrid zai sake karawa da na FC Barcelona kwana uku kacal bayan sun hadu a gasar cin Kofin Copa del Rey matakin kusa da na karshe. A wasan, Barcelona ce ta lallasa Madrid ta ci 3-0 bayan an yi kunnen doki 1-1 kimanin mako uku a filin wasa na FC Barcelona.  Yanzu dai FC Barcelona ta fitar da Madrid a wannan gasa inda ta kai wasan karshe a karo na 6 a jere. Sannan Barcelona ce ta fi kowane kulob yawan daukar wannan kofi, inda kawo yanzu ta dauka har sau 30 yayin da Madrid ta dauka sau 19.

Wasan na gobe zai gudana ne a filin wasan Madrid na Santiago Bernebeu da misalin karfe 6 da minti 45 na dare agogon Najeriya.

A wasa zagayen farko, FC Barcelona ce ta lallasa  Madrid da ci 5-1.

Kawo yanzu FC Barcelona ce take saman teburi a gasar da maki 57 sai Atletico Madrid ke biye da maki 50 sai Real Madrid a matsayin ta uku da maki 48 sai kulob din Getafe a matsayin ta hudu da maki 40.

Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil  don ganin yadda wasan zai kaya.