Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC za ta gurfanar da tsohon Akanta Janar na Kasa Ahmed Idris a gaban kuliya a ranar Juma’a.
Za a gurfanar da shi ne bisa tuhumarsa da almundahana da kuma aikata zamba cikin aminci na jimlar kudi har sama da Naira biliyan 109.
- Hatsarin mota: Mutum 30 sun kone kurmus a hanyar Zariya zuwa Kano
- Kowanne dan Najeriya yanzu yana da hannun jari a NNPC – Mele Kyari
EFCC za ta gurfanar da Ahmed Idris ne shi da wandada ake zargi a gaban Mai Shari’a A.O Adeyemi Ajayi na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.
Sauran wadanda ake tuhumar da aikata laifin da shi sune Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman da kuma kamfanin hada-hadar kayan noma da ke Gezawa.
Hukumar ta EFCC na tuhumarsu ne da aikata wasu laifuka guda 14 ciki har da sata, da kuma zamba cikin aminci na kudin da ya kai jimlar Naira biliyan 109.
Bayanin tuhumar na cewa Ahmed Idris ya yi amfani da matsayinsa na Babban Akanta na Kasa, tare da hadin bakin wandanda ake zargi, suka damfari gwamnatin tarayya Naira Biliyan 84 tsakanin watan Fabarairu zuwa Nuwamba na 2021
Sannan kuma tare da hadin baki da Kamfanin Godrey Olusegun Akindele, tsohon akantan ya aikata zamba cikin aminci wanda laifi ne a karkashin sashe na 315 na kundin Penal code, da kuma dokoki masu lamba 532 na Tarayyar Najeriya na shekarar 1990.