Hukumar Yaki da Cin Hanci da Ta’annutin Kudi ta EFCC ta ce hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta ki mika jami’anta don su amsa tambayoyi kan binciken badakalar makamai.
A sanarwar da Mai Magana da Yawun Hukumar EFCC, Wilson Uwujare ya raba wa manema labarai ya ce ba sabon abu ba ne hukumar EFCC ta gayyaci jami’an tsaro don bayar da bahasi kan binciken da hukumar take yi.
Ya bayyana cewa akwai matakan yin hakan “Daya daga cikin matakan yin hakan shi ne hukumar ta rubutawa shugaban hukumar tsaron ta mika jami’an da ake son a yi wa tambayoyin”.