✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC ta gayyaci Bukola Saraki kan zargin rashawa

Shekara uku ke nan bayan Kotun Koli ta wanke Saraki daga wasu zarge-zarge.

Rotanni sun nuna Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta gayyaci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi a ranar Asabar.

Wasu majiyoyi sun ce EFCC ta gayyaci tsohon Gwamnan na Jihar Kwara ne bisa zargin wawure kudaden gwamnati ta hanyar amfani da wasu mukarrabansa da kamfanoninsu.

Amma wata majiya a EFCC ta ce hukumar ta gayyaci Bukola Saraki ne zuwa ofishin nata, kuma yana can tun wajen Azahar na ranar Asabar.

Wani babban jami’in hukumar ya ce hukumar ta gayyaci Saraki ne a cikin makon nan  kuma ya ba ta tabbacin cewa zai amsa gayyatar a ofishinta idan ya zo wani daurin aure a Abuja ranar Asabar.

Da yake tababtar da zuwan tsohon gwamnan ofishin EFCC, wani jami’in hukumar ya ce bahasi hukumar take nema daga gare shi a wani bincike da ta take yi kan magajinsa a Jihar Kwara, Abdul-Fatah Ahmed wanda kuma makusancinsa ne.

“Asali ba Sarki hukumar take bincika ba, tsohon Gwamnan Jihar Kwara Abdul-Fatah Ahmed ake bincike a kai, amma ta kama sai an gayyaci Sarakin domin ya yi karin haske a kan wasu abubuwa”, inji jami’in.

Ya ce a lokacin da yake gwamna, Abdul-Fatah Ahmed da wasu mukarraban Saraki sun aiwatar masa da wasu ayyuka a Jihar ta Kwara.

Duk kokarinmu na samun karin bayani daga kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, hakarmu ba ta cim ma ruwa ba.

A lokacin da yake Shugaban Majalisar Dattawa daga shekarar 2015 zuwa 2019, Bukola Saraki ya shafe shekara uku yana fuskanatar shari’a kan zargin rashawa da kuma karya wajen bayyana kadarorinsa.

Amma a shekarar 2018 Kotun Koli ta wanke shi.

Sabuwar dambarwar dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura da mai dakinsa,  Mairo, kan facaka da kudaden gwamnati.