✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama shugabannin Kananan hukumomin Kwara 16

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa EFCC ta kama wasu shugabannin kananan hukumomi 16 na jihar Kwara, saboda zarginsu…

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa EFCC ta kama wasu shugabannin kananan hukumomi 16 na jihar Kwara, saboda zarginsu da yin facaka da wani bangaren kudin gwamnati da ya kai Naira biliyan hudu. Sannan sai karkatar da kudin harajin jihar na kashi 10 cikin 100.

A yanzu haka dai wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi a hannun hukumar EFCC.

Shugabannin da ake tuhuma sun hada da: Risikat Opakunle, Saidu Yaru Musa, Umar Belle, Ayeni Dallas, Fatai Adeniyi Garba, Lah Abdulmumeen, Raliat Funmi Salau, Aminat Omodara, da Muyiwa Oladipo.

Sauran su ne; Oladipo Omole, Abdullahi Abubakar Bata, Saka Eleyele, Lateef Gbadamosi, Oni Adebayo Joseph, Omokanye Joshua Olatunji da Jibril Salihu.

Jim kadan, Hukumar ta EFCC ta yi nasarar kama wasu matasa 200 ‘yan damfarar yahu-yahu duk a jihar.