Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama gwamman masu sana’ar POS a Jihar Ondo a karshen mako.
An kama mutanen ne saboda zarginsu da badakalar sayar da sabbin kudade a kan farashi mai dan karen tsada.
- Akwai maganin ciwon ido na jabu a kasuwannin Najeriya – NAFDAC
- An kama mai gadi kan yi wa ’yar makwabcinsa fyade a Abuja
Aminiya ta gano cewa jami’an hukumar wadanda ke sanye da fararen kaya sun yi wa Akure, babban birnin Jihar kawanya ne a kokarinsu na kama mutanen a manyan kasuwannin birnin.
Bayanai dai sun nuna yawancin mutanen sun rika cin karensu ba babbaka, inda suka rika sayen takardun kudaden daga hannun bankuna suna sayar da su ga mutane a kan farashi mai tsada.
Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa Aminiya da kamen a wani samame da suka kai Jihar.
Ya ce kai samamen ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu ne kan yadda galibin masu sana’ar ke boye sabbin kudaden don kuntata wa jama’a.
Ya ce, “Wani gagarumin samame ne muka gudanar a Akure da wasu sassan Jihar. Mun sami bayanan da ke nuna masu POS na tatsar mutane a kan sabbi da tsofaffin kudi.
“Mun yanke shawarar yi musu dirar mikiya ne musamman a cikin manyan kasuwannin birnin, inda a nan ne wannan dabi’ar ta fi kamari.
“Za mu shafe tsawon mako guda muna wannan aikin, kuma muna yin shi ne domin mu kawo gyara kan yadda kudade za su wadata a Jihar da ma kasa baki daya,” in ji jami’in.