Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode.
Rahotanni sun ce ofishin hukumar da ke Jihar Legas ne ya cika hannu da shi kan zargin cuwa-cuwar takardun bogi.
- Farashin man fetur zai iya kaiwa N340 a 2022 – NNPC
- Abin da ya sa muka ragargaza babura 482 – Gwamnatin Legas
Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan ta wayar salula da yammacin Talata
EFCC dai na zargin Fani-Kayode, wanda kwanan nan ya koma jam’iyyar APC mai mulki, da yin cuwa-cuwa a takardar asibitin da ya gabatar ta karya don kauce wa gurfana a gaban kotu.
Daga bisani dai hukumar ta wuce da shi zuwa ofishinta na shiyya da ke Legas don ya amsa tambayoyi da wajen misalin karfe 1:05 na rana bisa rakiyar lauyoyinsa.
Sai dai Wilson Uwujaren bai tabbatar wa da Aminiya ko za a sake shi a cikin daren Talata ko kuma zai kwana a hannun hukumar ba.
“Tabbas yana hannunmu, amma ba zan iya tabbatar da ko za mu sake shi cikin daren nan ko kuma a’a ba,” inji kakakin.
Idan za a iya tunawa, dan siyasar dai na fuskantar tuhuma ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan zargin badakalar Naira biliyan 4.6.
Ana tuhumarsa ne tare da tsohuwar Ministar Kudi, Nenadi Usman da wasu mutum biyu kan zarge-zarge guda 14 masu nasaba da zambar kudade, cin amana da kuma damfara.
A zaman kotun na karshe dai a a ranar 13 ga watan Oktoban 2021, alkalin kotun ya ci shi tarar N200,000 saboda kin bayyana a gaban kotun.