✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC ta kai samame Kasuwar Wapa, ta cafke mutane 8

’Yan kasuwar Wapa da dama sun rufe shagunansu.

Hukumar Hana Yi wa Tattalin Arziki Zagon-kasa a Najeriya (EFCC), ta kama masu canjin kudaden ketare takwas a wani samame da ta kai Kasuwar Wapa da ke Kano.

Aminiya ta gano cewa jami’an EFCC sun dirarwa kasuwar ce da Yammacin ranar Talata, inda suka kama mutanen, lamarin da ya hargitsa kasuwar.

Guda daga cikin ’yan kasuwar da Aminiya ta tattauna da shi ya ce lamarin ya sanya ’yan kasuwar da dama rufe shagunansu.

Wani ma da ya nemi a sakaya sunansa ya ce za su dakata da bude shagunansu a kasuwar, har sai al’amura sun daidaita, kasancewar ba wannan ne karon farko da EFCC ta yi irin haka ba.

“Duk lokacin da aka yi makamancin wannan samamen, farashin Dala tashi yake yi sosai. Yanzu daga N835 da muka sayar da ita jiya, har ta kai N845 yau da haka ta faru.

“To a makon da ya gabata ma kwata-kwata N780 ce, amma saboda gwamnati ta boye dalar shi ya sa take kara hawa, amma sun bar jaki sun zo suna dukan taiki.

“Mu ma da tsada muke sayo ta, don haka dole mu kara ribarmu. Idan ana so Dala ta sakko, kwai gwamnati ta fito da ta hannunta”, in ji shi.

Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a sakaya sunasa ya ce samamen guda ne daga shirye-shiryen hukumar na mara wa Gwamantin Tarayya baya don kawo karsen hauhawar farashin Dalar.

Ya kuma ce baya ga haka, hukumar ta lura da yadda masu damfarar mutane kudi ke amfani da masu canjin ta bayan fage suna halasta kudaden haram, musamman dalilin sauya fasalin Naira da za a yi.

Wannan dai na zuwa ne kawanki kadan bayan EFCC din ta kai samame kan kasuwar ’yan canjin a Abuja.