✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC ta girke jami’ai a wurin zaben dan takarar shugaban kasa na APC

APC na gudanar da taron zaben dan takararta na kujerar shugaban kasa a Abuja

Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arziki ta Kasa (EFCC) ta girke jami’anta domin sanya ido kan zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ke gudana a Abuja.

Wakilan Aminiya sun ga jami’an na EFCC sun ga yadda jami’an hukumar suke kai-komo a wurin taron da ke gudana a Dandalin Eagles Square a birnin Abuja.

Duk da cewa taron bai kankama ba, ana ganin hallarar jami’an hukumar a wurin taron na da nasaba da zargin hada-hadar kudade da sunan sayen daliget a lokacin tarukan zaben ’yan takara.

A ranar Talata ne dai jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya take fara gudanar da babban taronta da zaben dan takararta na kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Kawo yanzu dai ana ta kiki-kaka kan wanda jam’iyyar za ta fitar, inda gwamnonin Arewa ke son a bai wa yankin Kudanci, a yayin da wadansu daga cikin masu neman kujerar daga yankin Arewa suka ce ba za ta sabu ba.

Ya zuwa wannan lokaci dai sai sake lale jam’iyyar take yi a kan batun fitar da dan takara babu hammaya, lokacin fara gudanar da zaben kuma sai kara karatowa yake ta yi.