Bayan shafe awoyi ana wasan buya, daga karshe dai jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC sun cafke tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.
Wakilinmu wanda ke bibiyar lamarin ya ce an kama dan siyasar, wanda Sanata ne mai ci, kuma daya daga cikin masu neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC wajen misalin karfe 6:47 na yammacin Talata, a gidansa da ke Abuja.
- Kotu ta tabbatar da na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban PDP a Kano
- IPOB ta kashe mai ciki da wasu ’yan Arewa 11 a Anambra
An dai yi harbe-harbe domin tarwatsa magoya bayan da suka yi dandazo a kofar gidan tsohon Gwamnan, kafin daga bisani a sami nasarar kama shi.
Tun da farko dai jami’an hukumar sun lashi takobin cewa ba za su bar gidan ba sai sun tafi da shi.
A cewar wani jami’in hukumar, za su ci gaba da tsare shi a hedkwatar EFCC har zuwa nan da ranar 30 ga watan Mayun 2023, ranar da za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ana dai tuhumar Sanata Rochas ne da karkatar da wasu makudan kudade lokacin da yake jan ragamar Jiharsa ta Imo.