✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC na neman AA Zaura kan zargin damfara

Hukumar na neman dan siyasar ne domin gurfanar da shi a kotu kan zargin damfara ta Dala miliyan 1.3.

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki EFCC ta ce tana neman dan takarar Sanata na Jam’iyyar APC a Jihar Kano Abdulkareem Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura.

Hukumar na neman dan siyasar ne domin gurfanar da shi a kotu kan zargin damfara ta Dala miliyan 1.3.

EFCC na so ta sake gabatar da shi ne gaban kotun daukaka kara wadda ta soke hukuncin baya da ya wanke AA Zaura daga zargin.