Kwamitin Lura da Harkokin Wuta na Majalisar Dattawan Najeriya ya bayyana aikin gina madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki na Mambila a matsayin fata kawai duk da biliyoyin naira da aka kashewa aikin.
Ministan Wutar Lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu shi ne ya bayyana haka duk da dimbin kudin da ake ware wa aikin a kasafin kudi na shekaera-shekara da ya kai biliyoyin naira.
Aminiya ta ruwaito Ministan na fadar hakan ne yayin da ya ce Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasar Zagon-kasa, EFCC na gudanar da bincike kan aikin.
Batun ya taso ne yayin zaman kare kasafin kudi na 2023 ranar Talata tare da Ministan Lantarki da sauran hukumomi da ke karkashin ma’aikatar.
Shugaban kwamitin Sanata Gabriel Suswam (PDP, Benuwe), ya ce abin takaici ne duk da dimbin kudin da aka yi ta ware wa aikin wanda tun shekara 30 baya aka tsara shi, ba abin da aka yi a aikin.
Sanatan ya ce tun 2017, ake ware wa aikin na Mambila kudi amma ba abin da aka yi duk da matsin lambar da Majalisun Dokoki da kuma ’yan Najeriya suke yi.
Aikin madatsar ruwan wanda zai samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050, idan aka kammala shi zai kasance mafi girma a Najeriya sannan kuma daya daga cikin mafiya girma a Afirka.