Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce ba ta da wata matsala da masu amfani da kudin Crypto a Najeriya, matukar sun yi ta halastacciyar hanya.
Daraktan sashen ayyuka na Hukumar Abdulkareem Chukkol ne ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin mutane a shafin hukumar na Twitter ranar Laraba.
- Dagaci ya rasa rawaninsa a Kano saboda badakalar filaye
- Zaben fid da gwanin PDP: Daliget 2 ne suka zabi Shehu Sani a Kaduna
Sai dai yace hukumar ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen cafke wadanda ke amfani da hanyar wajen damfarar mutane.
“Crypto yanzu abin da duniya ke yayi ne da ba mu da ikon hana mutane su yi amfani da shi, duk da haka muna nan muna horar da jami’anmu kan harkar, domin sanin yadda za su tafiyar da lamarinta idan ya zo gabanmu,” inji Abdulkareem.
Da yake amsa tambaya kan yadda hukumar ke gano laifuka su bincika, ya ce “Ba iya korafin rubutu kadai muke bibiya ba, muna samun rahotannin sirri kuma take mu yi aiki akan wadanda suka dace.
“Hukumar mu ta EFCC na da manhaja da za a iya kawo mana korafi ta ciki, kuma mun samu dubban korafe-korafe a ‘yan watannin baya, kuma mun dawo da dukiyoyin mutane da dama gare su.”