✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Eden Hazard ya ki sabunta kwantaraginsa da Chelsea

Rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun nuna dan kwallon Chelsea Eden Hazard ya ki yarda ya tsawaita kwantaraginsa da kulob din Chelsea duk da…

Rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun nuna dan kwallon Chelsea Eden Hazard ya ki yarda ya tsawaita kwantaraginsa da kulob din Chelsea duk da tayin da kulob din ya yi masa na kara masa albashi zuwa Fam dubu 300 a mako kwatankwacin Naira Miliyan 141 a matsayin albashi.

dan kwallon wanda yanzu saura shekara biyu da rabi kwantaraginsa ta kare da kulob din Chelsea, kulob din ya fara yunkurin tsawaita masa kwantaragi ne ganin yadda kulob da dama ke rububi a kansa ciki har da kulob din Real Madrid na Sifen.

Sai dai Eden Hazard ya ce ba zai yi gaggawar tsawaita kwantaraginsa da kulob din ba, hasalima sai an gama kakar wasa ta bana kafin ya yanke hukunci.

Kulob din Real Madrid dai ya dade yana zawarcin Hazard kuma alamu sun nuna dan kwallon yana da sha’awar komawa can idan ya samu dama.

Eden Hazard dai tauraruwarsa na haskakawa a kakar wasa ta bana, inda kawo yanzu ya zura kwallaye 9 a raga a gasar rukunin firimiyar Ingila.

Haka kuma an ruwaito Madrid tana zawarcin golan Chelsea Thibaut Courtios da ake ganin kwantaraginsa za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana.