✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta bukaci a bi doka yayin da shugabannin Afirka suka taya Shugaba Buhari murna

Wadansu daga cikin shugabannin Afirka sun taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zabe karo na biyu. Rahotanni sun ce Shugaba Nana Koffi-Addo na Ghana…

Wadansu daga cikin shugabannin Afirka sun taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zabe karo na biyu.

Rahotanni sun ce Shugaba Nana Koffi-Addo na Ghana da Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou da Macky Sall na Senegal sun mika sakon taya murna ga Shugaba Buhari.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyata ya ce cin zaben da Buhari ya yi alama ce ta yadda ’yan Nageria suka amince da jagorancinsa domin ya dora kan ayyukan da yake musu domin ci gaban kasa kamar yadda BBC ya ruwaito.

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan Mufti Menk ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zaben na bana.

Malamin wanda dan asalin kasar Zimbabwe ne ya yi addu’ar “Allah Ya kare Shugaban, Ya kuma ci gaba da yi masa jagora a dukan al’amuransa.”

Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Kungiyar Tarayyar  Afirka ta AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya, sun yi kira ne ga jam’iyyun siyasa da wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben Shugaban Kasar da aka sanar ba,  su bi hanyar da dokar Najeriya ta shimfida wajen bin kadinsu.

Kungiyoyin da Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana haka ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar kamar yadda Muryar Amurka ta rawaito.

Sanarwar ta ce, “Muna kira ga dukan jam’iyyu da wadanda ke da korafi, su bi hanyoyin da doka ta shimfida domin bin kadinsu, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma kamar yadda aka rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta ranar 13 ga watan Fabrairru,” sanarwar ta nuna.