✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Eboue ya sake aure bayan tsohuwar matarsa ta tsiyata shi

Tsohon dan kwallon Arsenal Emmanuel Eboue ya sake sabon aure a kasar haihuwarsa Kwaddebuwa. Eboue wanda a bara ne ya rabu da tsohuwar matarsa Aurelie…

Tsohon dan kwallon Arsenal Emmanuel Eboue ya sake sabon aure a kasar haihuwarsa Kwaddebuwa.

Eboue wanda a bara ne ya rabu da tsohuwar matarsa Aurelie Bertrand ’yar asalin Beljiyam da hakan ta sa ya shiga mawuyacin hali ya sake yin aure ne a karshen makon jiya.

Misis Aurelie Bertand dai ta haifi ’ya’ya uku tare da Eboue kafin ta kai shi kara inda kotu ta raba aurensu kuma ta mallaka wa tsohuwar matar daukacin dukiyarsa tare da yaran da suka haifa.

Eboue da tsohuwar matarsa da ta tatike shi

Hakan ya sa Eboue ya tsiyace ya koma kwana a wani garejin mota da abokinsa ya taimaka masa a Ingila saboda rashin kudin da zai iya kama haya.

Jim kadan bayan labarin tsiyacewarsa ya bazu a kafofin watsa labarai  ne sai kulob din Arsenal ya tausaya wa Eboue inda ya dauke shi aiki don ya saukaka masa kuncin rayuwa.

Eboue wanda ya yi wasa a kulob da dama a Nahiyar Turai, ya fi shahara ne a lokacin da yake yi wa kulob din Arsenal na Ingila wasa.

Rahotanni sun nuna kafin Eboue ya auri matarsa ta farko, ya yi soyayya da amaryar da ya aura yanzu wato Stephanie Boedé tun kafin ya tafi Turai don yin kwallo.

Sai dai bayan ya tafi Turai ne sai ya hadu da Aurelie Bertand, Baturiya ’yar asalin Beljiyam inda ya canja shawara kuma ya aure ta.  Bayan sun haifi ’ya’ya uku sai sabani ya shiga tsakaninsu inda ta kai shi kara gaban alkali. Kotu ta zartar da hukuncin mallaka wa tsohuwar matarsa daukacin gidaje da dukiyar da ya mallaka a Turai  tare da ’ya’yan da suka haifa wanda hakan ya sa Eboue ya tsiyace.

Bayan Eboue ya dan farfado ne ya yanke shawarar komawa Kwaddebuwa inda ya auri tsohuwar budurwarsa Stephanie Boedé kuma an yi shagali a bikin ba tare da  almubazzaranci ba.

Rahotanni sun ce tuni tsohuwar matarsa ta koma Beljiyam don ci gaba da rayuwa tare da ’ya’yanta uku da suka haifa da Eboue da kuma daukacin dukiyarsa da kotu ta mallaka mata.