✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dusar kankara ta kashe mutum 3 a Spain

Dusar kankarar ta hana mutane fita daga gidajensu a wasu garuruwan kasar.

Akalla mutum uku ne suka rasa rayukansu, a kasar Spain, sakamakon dusar kankara da rabon  a yi irinsa kasar tun shekara 40 da suka gabata.

A ranar Juma’a kasar ta Spain ta fara fuskantar matsalar zubowan dusar kankara mai yawan gaske.

Wannan ita ce mafi yawa da kasar ta taba fuskanta tun daga shekarar 1971.

Dusar kankarar ta rufe manyan titunan babban birnin kasar, Madrid da wasu birane da ke kasar.

Hukumar kula da yanayi ta kasar, ta yi hasashen za a sake samun karin kaso 20 na zubar dusar kankarar daga ranar Asabar.

Sai dai Fira Ministan kasar, Pedro Sanchez, ya yi kira ga ‘yan kasar da su zauna a gida tare da bin umarnin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar.

Fira Ministan ya yi wannan kira ne ta shafinsa na twitter a yammacin ranar Juma’a.

Tun a ranar Juma’a aka rufe filin jirgin saman Barajas, da ke birnin Madrid.

Hukumar ba da agajin gaggawar kasar da ke birnin Madrid, ta bayyana hotunan yadda take aikin ciro ababen hawan da suka makale a dusar kankarar.