✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duniyar Ma’aurata: Matakan cim ma nasarar daren farko

Ga ci gaban bayani kan ladubban daren farko domin sabbin Ma’aurata.

Assalamu alaikum. Barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban daren farko domin sabbin Ma’aurata.

Muhimmancin Daren Farko

Ana iya cewa daren farko shi ne daren da ya fi kowane dare muhimmanci a rayuwar ma’aurata, daren da za su bude wani sabon shafi na rayuwa a cikinsa, don haka yana da matukar alfanu yin duk irin shirin da ya kamata domin samun nasararsa, domin kuwa nasara ko rashin narasar wannan dare zai yi matukar tasiri a cikin irin yadda rayuwar ma’aurata za ta kasance.

Shirye-shiryen gabatowar daren farko

Shirin farko da ya kamata ma’aurata su yi shi ne shiri na kyautata niyya, domin: Dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, kuma irin niyyar da ka yi, irin abin da za ka samu. Niyya mai kyau ita ce a kudurta cikin zuciya, babban dalilin yin auren nan don Allah ne, saboda Allah ne, don cika addini, don kare kai daga zina da kannenta, don samun zuriyya dayyaba da sauran kyawawan kudurori makamanta haka.

Kar a kudurta niyyar aure saboda son juna kadai, ko saboda wanda za a mallaka ya mallaki wani abu da ake so kamar kyau, matsayi ko dukiya. Shiri na biyu shi ne kokarin tafiyar da kunya tsakanin ma’aurata.

Wasu daga cikin makaranta maza sun aiko da sakonni suna neman bayanin yadda za su yi su tattauna maganar ibadar aure da matan da za su aura, domin lurar da suka yi da tsananin kunyarsu.

Kasancewar sababbin ma’aurata duk baki suke ga wannan harka ta ibadar aure, dole daman ya kasance akwai kunya da ’yar fargaba game da daren. Don samun cikakkiyar nasarar daren farko, sai ma’aurata sun rage jin kunyar da ke tsakaninsu, ya kasance suna tattaunawa kan batun ibadar aure da yadda suke fatan daren farkon su ya kasance.

Da kuma dokinsa da sa kyawawan tunani cikin zuciya game da shi tun kafin zuwan ranar. A nan aikin ango ne ya runka bi a hankali, cikin wasa da raha da zolaya, ta hanyar amfani da kalmomi makimanta ba masu nauyi ba, kuma ya kasance suna cike da shauki, har ya ga ya zakulo amaryarsa ta rage jin kunya, in ma dai ba ta daina din ba, fada matan zai sa ta zama cikin sani abin da ka iya faruwa.

Haka kuma yana da kyau ma’aurata su nema tare da karanta littattafai da sukai bayani kan ilmin ibadar aure don su fahimci abin sosai.

Shirya jiki da jini: Domin dai jiki da jini kamar inji ne da fetur din gabatar da ibadar aure don haka yana da alfanu ga ma’aurata su inganta lafiyar jikinsu da ta jininsu ta hanyar cin abinci masu kyau da gyara jiki, musamman ganyayyki da ’ya’yan itatuwa da yawan motsa jiki da sauran shirye-shirye makamantan wadannan.

Yin kyakkyawan zato game da juna: Ango ya sani, abubuwa da yawa na iya balle murfin budurcin ’ya mace, daga cikin su akwai jinin haila mai nauyi ko hawa sama ko tsalle-tsalle ko hawan keke doki ko jaki da sauransu. Don haka, haramun ne ya kawo wani mummunan zargi game da matarsa har in ya sameta ba da murfin budurcinta ba.

Kudurta cewa: Ana iya samun Matsala! Ma’aurata su sani cewa ba lallai ba ne su samu nasara a daren farkonsu domin gajiyar hada-hadar biki da fargabar yin wani muhimmin abu a karo na farko na iya haifar da kaduwar jiki har ta sa Ango ya ji ya kasa, don haka ba lallai ba ne dole sai an gabatar da ibadar aure a daren farko, in aka daga shi zuwa wani daren, bayan jiki ya huta, abin ya fi kayatarwa ma.

Sannan ga sabon angon da ya san ya yi sabo da zinar hannu, ya kamata ya yi kokarin dainawa akalla wata uku kafin daren farko, kuma ya bi duk shawarwarin da suka zo a wannan fili kan hanyoyin rabuwa da zinar hannu don magance ta kafin ranar, don in ba haka ba akwai yiwuwar samun matsala.

Sababbin ma’aurata su sani, haramun ne gare su yin tunane-tunanen alfasha, kallon finan finan alfasha ko karanta littattafan alfasha, wai da nufin su koyi ibadar aure, kuma wadannan wasu abubuwa ne da ke bata rayuwar aure. Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.