A makon da ya gabata ne wata dungiya mai zaman kanta, Gidauniyar Zaman Lafiya (GPF) ta ziyarci garin Kafanchan da ke kudancin Kaduna inda ta gana da dungiyoyin al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda za a samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Taron, wanda aka gudanar da shi a dakin taro na hotel din New Choice, ya samu halartar dukkanin mutane da dungiyoyin da aka gayyata.
A cikin jawabinas, Rabaran Joseph Hayab, ya bayyana talauci da rashin aikin yi da matsalar kiran wasu badi wasu kuma ‘yan dasa da kalaman tunzura da shugabannin addini da na siyasa da sarakuna ke yi wa jama’arsu a matsayin wasu daga cikin dalilan da ke haddasa fitina a yankin. Inda yayi kira ga mahalarta taron kan muhimmancin zaman lafiya.
Shi ma a nasa jawabin, Sheikh Halliru Maraya, ya bayyana yankin kudancin Kaduna da cewa yanki ne da Allah ya huwace mata arzidi mai dimbin yawa amma rashin zaman lafiyar yankin ya sa mutanen yankin da ma na jihad a dasa baki daya sun kasa cin gajiyar arzidin.
“Na yi imani cewa babu daya daga cikinku wanda rikice-rikicen nan bai shafa ba ko da kai tsaye ko ta wata hanyar. Yaushe za ku daina kashe-kashen rayuka da dona dukiyoyi da wuraren ibada da na kasuwanci? Idan har ba mu koma mun yi rido da karantarwar da ke cikin addinanmu ba babu ranar da za a daina zubar da jinin juna domin addini hanya ce ta kyautata alada tsakanin halittu da mahalicci da kuma tsakanin halittu su ya su. Allah ya halicce mu duka ta hanyar Adamu da Hauwa’u don haka dukkanmu iyali daya ne dardashin Ubangiji.”
dunngiyoyi da dama da suka hada da dungiyar mutanen kudancin Kaduna (SOKAPU) da dungiyar Fulani Makiyaya (Miyetti Allah) da dungiyar kiristoci ta dasa da takwararta na musulmai (CAN/JNI) da dungiyar Mobgal Fulbe da kuma al’ummun da suka wakilci masarautun Godogodo da Kaninkon da Dangoma da Jaba da Numana da Chawai da Bajju da Kagoma inda aka bada dama ga dukkanin dungiyoyin suka bayyana ra’ayinsu kan hanyar da ya kamata a bi don samar da mafita kan rikice-rikicen day a addabi yankin.