Guda daga cikin fasinjojin jirgin kasan da suka kubuta ya ce dukan da aka yi musu a bidiyon da ’yan bindigar suka fitar a karshen mako somin tabi ne a kan abin da wadanda suka rage a hannunsu za su fuskanta.
Fasinjan mai suna Hassan Usman ya ce da farko ’yan bindigar ba sa dukan su, amma hana ’yan uwansu kai kudin fansarsu da jami’an tsaro suka yi ya fusata su, suka fara dukansu babu kakkautawa.
- Yadda ’yan daba suka hargitsa unguwar Kurna a Kano
- Zanga-zangar Kungiyar Kwadago ba za ta shafi sufurin jirage ba —NUATE
Cikin wata tattaunawa da kafafen yada labarai daban-daban, Hassan ya ce, “Ni yanzu tausayin ’yan uwana da na baro a can nake ji, saboda wannan dukan somin tabi ne kan abin da za su fuskanta.”
Hassan, shi ne mutumin da aka gani a bidiyon da ’yan bindigar suka fitar yana bayani yana rokon a kawo musu dauki.
“Kamar yadda na fada a wancan bidiyon, yanzu ma zan maimaita, kungiyoyi da kasashe masu fada a ji na duniya su taimaka su kubuto da sauran fasinjojin nan, domin gwamnatin kasarmu ta gaza, kuma ba ta da aniyar yin hakan.”
Sai dai ya ce duk da haka abincin da ’yan bindigar ke ba su sai hamdala, suna kokarin ciyar da su, saboda har raguna da shanu suke yanka musu.
“Ko a jiya ma sai da aka yanka mana sa muka ci. Alhamdulillah”, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa a baya suna kwana ne a dandagaryar kasa, amma daga bayan suka ba su tabarmi, tare da kafa musu tantuna bayan faduwar damina.
Da yake amsa tambayar kafar yada labarai ta BBC kan ko biyan kudin fansa ne ya sa aka sake su, ya ce ba shi da masaniya kan hakan.
Hakazalika ya ce yanzu haka dai ba zai iya gane dajin da aka killace su a ciki ba.
A ranar Litinin ne dai ’yan binidgar suka sako Hassan Usman, tare da wasu mutane biyu namiji da mace, daga cikin ragowar mutane 43 da ke ’yan ta’addar.
A wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa, Hassan ya nuna murnarsa ga ’yan uwa da abokan arzikin da suka jajirce wajen ganin ya kubuta, inda har ya fashe da kuka yayin da yake godiyar.
Daga nan ne kuma ’yan uwan nasa suka sanya shi a mota aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Sani Usman, dan uwa ne ga Hassan Usman, ya kuma ce akwai alamun rashin lafiya a tare da dan uwan nasa, baya ga rashin ruwa a jikinsa, shi ya sa ma suka kai shi asibitin.
“Muna godiya ga duk ’yan Najeriya, musamman ’yan jarida, sun nuna mana tausayi da kauna sosai. Muna godiya.
“Kuma muna fatan gwamnati za ta yunkuro domin ceto sauran fasinjoji 40 din da har yanzu ke hannun ’yan bindigar.”