✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk layin wayar da aka toshe ba za a bude ba sai…

Hukumar NCC ta gargadi jama'ar Najeriya kan shafin intanet na bogi da ake yadawa cewa yana layukan da aka toshe

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin cewa duk layin waya da aka tsohe, ba za a bude shi ba sai tare da lambar shaidar dan kasa (NIN).

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ce ta sanar da hakan, bayan umarninta na makon jiya ya sa kamfanonin sadarwa sun toshe miliyoyin layukan waya da ba a hada su da lambar NIN ba.

Sanarawar ta safiyar Talata ta ce, “Hukumar NCC na sanar da masu amfani da layukan sadarwa cewa kamfanonin sadarwa ba za a bude duk layin wayan da aka toshe ba sai idan har an hada layin da lambar NIN ta mai shi”.

Hukumar ta bayar da umarnin rufe layuka marasa lambar NIN ne bayan cikar wa’adin da ta bayar, tana mai cewa yin hakan shi ne abin da ya dace domin inganta tsaron Najeriya da kare jama’a daga masu damfara ta intanet da kuma inganta ayyukan ci gaban kasa.

NCC ta ce karin bayanin ya zama dole ne saboda labaran karya da ake ta yadawa game da wani shafin intanet na bogi (mai suna https://bit.ly/NCC-Sim-Unbar-Gov-Ng) a kafofin sadarwa da shafukan intanet cewa ana bude layukan da aka toshe a shafin.

Hukumar ta bayyana cewa karya ce tsagwaronta ake yadawa a sakon da ke yawo cewa idan mutum ya shiga adireshin shafin bogin da ake riya cewa nata ne, za a bude mishi layin da aka rufe ba sai ya hada da lambar NIN ba.

Ta ce, “Wannan sakon karyar da aka sanya wa hoton tambarin hukumarmu, yana ikirarin cewa idan aka shiga adireshin mutum zai iya bude layinsa da aka toshe ko babu lambar NIN.

“To jama’a su sani cewa NCC ba ta taba bayar da sanarwa ko nuna alama cewa za a iya bude layin da aka toshe ba tare da hada shi da NIN ba, saboda haka jama’a su yi hattara da masu yada wannan ji-ta-ji-ta.”

Ta kara da cewa duk wanda aka toshe wa layi, yana iya ziyartar ofishin kamfanonin sadarwar da ke da lasisi, ya hada lambar NIN dinsa da na wayarsa ta kafofin da kamfanonin suka samar.