Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya umarci kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da su mayar wa fasinjoji kudin tikitinsu muddin aka samu jinkirin awa biyu jirgi bai tashi ba.
Ministan ya bayar da umarnin haka ne a ranar Alhamis, yayin wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa duk mako a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.
A yayin taron ne Ministan ya zayyano wasu daga cikin hakkokin fasinjan jiragen sama, inda ya kuma shawarce su a kan neman hakkokin a duk lokacin da aka tauye musu.
A cewasa, “Game da jiragen cikin gida a duk lokacin da aka samu jinkirin na fiye da awa daya, kamfanin zai tanadar wa da fasinjojin abinci da ruwa da ba su damar kiran waya sau daya ko kuma sakon kar-ta-kwana ko na imel.
“Domin akwai bukatar kamfanin jirgin ya nemi afuwar fasinjojin ta hanyar aike musu da sakon kar-ta-kwana ko na imel da cewa ‘muna neman afuwarku, za mu samu jinkiri na awa daya’.
“Idan kuma aka samu jinkiri na fiye da awa biyu, kamfanin zai mayar wa da fasinjojin cikakkun kudaden tikitin da suka saya.
“Jinkiri a tsakanin karfe 10:00 na dare zuwa 4:00 na Asuba kuma, kamfanin zai bai wa fasinjojin masauki a Otel da abinci da damar kiran waya sau biyu da sakon kar-ta-kwana ko imel da kuma jigilarsu ta zuwa da dawowa daga filin jirgin.”
A cewar Ministan, wadannan dokoki sun shafi har da jiragen ketare, kuma tuni ma’aikatarsa ta fara hukunta kamfanonin da suka take wa fasinjoji hakki.