✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk jam’iyyar da ta ba dan arewa takara a 2023 sai ta riga rana faduwa – Akeredolu

 “Kowa aka tsayar, matukar dan Kudu ne za mu mara masa baya, kawai dole ya zama dan Kudu,” inji shi.

Gwamnan Jihar Ondo, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya, Rotimi Akeredolu, ya yi gargadin cewa duk jam’iyyar da ta ba dan Arewa takarar Shugaban Kasa a 2023 sai ta fadi warwas.

Ya ce tuni Gwamnonin yankin suka bayyana matsayinsu karara kan cewa dole ne mulki ya koma yankinsu a 2023.

Akeredolu na wadannan kalaman ne ranar Talata a ofishinsa da ke Akure, babban birnin Jihar, lokacin da wata gamayyar kungiyoyin da ke hankoron ganin mulkin ya koma Kudu ta ziyarce shi, karkashin jagorancin Shugabanta, Dokta Pogu Bitrus.

Gamayyar ta kuma kunshi wakilcin kungiyoyin Ohaneze Ndigbo da Afenifere da kuma ta yankin Middle Belt.

A cewar Gwamnan, dukkan masu neman ganin Arewa ta ci gaba da mulki, na neman kawo wa kasancewar Najeriya kasa daya ne tangarda, wacce ya ce da ita ya yi amanna, muddin adalci ake magana.

Ya ce, “Mun yi taro kusan sau biyu zuwa uku, kuma a ciki mun bayyana matsayinmu karara cewa dole mulki ya koma yankinmu.

“Jam’iyyar da kawai take neman faduwa ce za ta tsayar da dan Arewa takarar Shugaban Kasa.

“Abin da kawai muke nema shi ne a kamanta yin adalci. Idan Arewa ta dana tsawon shekara takwas, kamata ya yi Kudu ita ma ta dana.

“Kowa aka tsayar, matukar dai dan Kudu ne za mu mara masa baya, kawai dai abin da muke cewa shi ne dole ya zama dan Kudu. Akwai mutanen da suka cancanta daga Kudu maso Kudu, da Kudu Maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma.

“Saboda haka, ni ma ina goyon bayan fafutukar da kuke yi. Matukar kuka yi kokari wajen wayar da kan matasa, sannan kuka hana yin magudin zabe, to za mu yi nasara,” inji Gwamna Akeredolu.

Tun farko da yake nasa jawabin, Shugaban gamayyar kungiyoyin, Dokta Pogu Bitrus, ya ce babban makasudin kafata shi ne ganin mulki ya koma Kudancin kasar nan a 2023.