✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Duk hukumar da ba ta kare kasafinta cikin kwana 7 ba ta rasa’

Majalisa ta ce idan wa'adin ya wuce ma'aikatun za su tashi a tutar babu.

Majalisar Dattawa ta ba wa hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya wa’adin mako guda su kare kasafin kudinsu na 2022 a gaban kwamitocinta, ko kuma su tashi a tutar babu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, shi ne ya bayar da wa’adin ga hukumomin gwamnatin da ba su riga sun kare kasafinsu ba a gaban kwamitocin majalisar da ke kula da ayyukansu.

Ya ce “An ba wa duk hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya wa’adin mako daya su zo su kare kasafinsu, kuma duk ma’aikata ko hukumar da ba ta yi hakan ba har wa’adin ya cika, to sai dai su hakuka.”

Da yake sanar da hakan a zaman Majalisar na ranar Talata, Sanata Ahmad Lawan ya ce mako dayan da aka bayar shi ne zai ba wa kwamitocin Majalisar damar kammala ayyukansu kan kasafin hukumomin sannan su mika wa Kwamitin Kasafi na Majalisar rahotanninsu.

“Daga makon nan da muke ciki kwamitocinmu za su fara kammala aikinsu kafin su gabatar da rahotanninsu ga Kwamitin Kasafi

“Mun ba wa kwamitocin karin lokaci ne domin su gana da hukumomin; Saboda haka idan muka tashi yau (Talata), muna sa ran kwamitocin su je su fara aikin kammala hada rahoton da ya rage a gabansu.

“Wannan mako za mu rika tashi karfe 1 na rana, ranar Alhamis zuwa Juma’a ko Asabar kuma kwamitocin za su yi aiki.

“Da yardar Allah kuma zuwa mako mai zuwa za a rufe aikin kare kasafin kudi na 2022.