✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk dan Adam yana yin kuskure

Assalam Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama domin in fadi ra’ayina a kan harkokin siyasar kasar nan masamman a kan wadanda suke…

Assalam Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama domin in fadi ra’ayina a kan harkokin siyasar kasar nan masamman a kan wadanda suke ganin cewa, gwamnatin APC ba ta yin kuskure ko kuma Shugaba Buhari ba ya yin kuskure duk abin da ya yi daidai ne. Ina ganin wannan ba karamin kuskure ba ne domin a yanzu haka a gaban wani idan ka ce gwamnatin Buhari ta yi kuskure sai ya ji kamar ka karyata Alkura’ani,  ba zai yiwu ba a ce mutum dan Adam ba ya yin kuskure masamman shugaban al’umma wanda idan ya yi wa wancan daidai to ya iya yi wa wani kuskure.  Don haka masu irin wannan tunani su canja.

Daga Hadi Tsohon Sarki Daura-08164205067.