✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk da katse layin sadarwa an yi garkuwa da mutum 9 a Kaduna

An yi garkuwa da mutane a kusa da makarantar sakandaren Bethel Baptist.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum tara a Jihar Kaduna, kasa da wata guda bayan gwamanti ta katse layin sadarwa a wasu sassan jihar.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin, a yammacin ranar Asabar.

“An yi garkuwa da su ne a kusa da Jakaranda kuma masu garkuwa da su na menan Naira miliyan 50‎; Jiya (Juma’a) aka kira ni daga kauyen,  inda ni da shugabanninsu muka gaya musu iya abin da za mu iya a irin wannan yanayi.”

An yi awon gaba da mutanen ne a kauyen Dangilmi da ke kusa da Makarantar Bethel Baptist inda a watan Satumba ’yan bindiga suka sace dalibai 121 a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Rabaran Hayab ya ce, “Dole yau (Asabar) na kira shugabannin makarantar na shaida musu cewa su dakatar da dukkannin abubuwan a makarantar tukuna.”