✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da kasafin N134bn, ’yan Majalisa na neman karin Kudade

Kasafin Malisun Tarayya ya ninku sau kusan shida a cikin shekara 18

’Yan Majalisar Tarayya na bukatar karin kudi, bisa hujjar karancin kudaden gudanar da harkokin bangaren Majalisar.

Tuni dai wasu ’yan Najeriya ke ganin kasafin Naira biliyan 134 da aka ware wa Majalisar a 2021 ya wuce kima suna kuma kokawa game da yadda ake kin bayyana abin da kasafin Majalisar ya kunsa.

Binciken Aminiya ya gano cewa kasafin Majalisar ya karu daga Naira biliyan 23.2 zuwa Naira biliyan 134 tsakanin shekarar a 2003 zuwa 2021.

A makon jiya ne tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya koka kan karancin kasafin yana neman a kara yawansa don gudana da harkokinta yadda ya kamata.

Y ace, “Gaskiya ba mu da kudi. Na fada a baya, ina kuma maimaitawa ba tare da fargaba ba.

“Wannan ita ce gaskiyar. Kasafin Majalisa a lokacin da farashin Dala yake N180 ya fi na yanzu, alhali kuma yanzu Dala ta haura N400. Darajar kasafin yanzu bai kai yadda yake shekaru 10 da suka gabata.”

Duk da kukan karancin kudaden, ’yan Majalisar na ci gaba da gudanarda da ayyukansu yadda aka saba, bambancin kawai shi ne yanzu an rage yawan ranakun zaman manyan zaurukanta.

Wani babban jami’i a Majalisar Tarayya ya bayyana mana a sirrance cewa da gaske akwai karancin kudaden, to da ya shafi gudanar zaman kwamitoci, wanda ya ce shi ke cin kudade.

“Zaman babban zauren Majalisa ba ya cin kudi kamar na kwamitoci da ake bukatar kudaden daukar hayar kwararru, sanya talla da sanarwa, sayen kayan makulashe da kuma alawus din mambo, bi.

“Idan har da gaske suke cewa Majalisar Tarayya ba ta da kudade, to abin da ya kamata su fara waiwaya ke nan,” inji shi.

 

Albashi mai tsoka

Baya ga albashi, kowane dan Sanata, ana biyan kowane sanata Naira miliyan 13 a wata, ’yan Majalisar Wakilai kuma kowannensu Naira miliyan 8.5 a wata.

A Majalisar da ta gabata ne Sanata Shehu Sani da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya a wancan lokacin ya bayyana abin da kowannensu yake samu.

Sanata Shehu Sani ya ce ana biyan kowannenu wadannan kudaden ne bayan albashinsu na Naira dubu dari bakwai da hamsin a kowane wata.

“Abin da nake nufi shi ne sai ka kawo shaidar yadda ka kasha kudaden (N13.5 da duk wata). Kudin da ba a bukatar bayanin abin da ka yi da shi shi ne N750,000.00.

“Shi kan shi kudin ayyukan mazabu ana ba da shi ne a matakin yanki yanki kuma kusan kowane dan majalisa na samun Naira miliyan 200; amma ba kudin ake ba ka ba.

“Za a ce maka kana da N200m a wurin wata hukumar gwamnati inda za ka gabatar mata da ayyukan da kake bukata a yi wadannan kudade. Ita wannan hukumar ce za ta aiwatar maka da wadannan ayyukan,” inji shi a shekarar 2018.

Abin da ya sa ba mu da kudi –’Yan majalisa

Wasu ’yan Majalisar Tarayya sun dora laifin rashin gudanar da ayyukanta a kan karancin kudade, rashin fitar da kudaden da kuma yawan matsin lamba daga jama’arsu da ke neman ’yan majalisa su yi musu ayyukan bangaren zartarwa bacin ayyukansu na yin doka.

Wani dan majalisar da ya nemi a boye sunansa ya ce duk da cewa kasafin kudin Majalisar na karkashin Gwamnatin Tarayya, fitar da kudaden samun tsaiko saboda gazawar hanyoyin tara kudaden hukumomin gwamnati.

“Yawanci ’yan Najeriya na kuskuren dauka cewa kasafin gudanar da majalisar na ’yan majalisar ne kawai. Shi ya sa wadanda muke wakilta suka dora mana nauyin abin da asalinsa na bangaren zartarwa ne,’ inji shi.

Wani dan majalisar ya fayyace cewa ba wai ’yan Majalisar Tarayya a daidaikunsu ba su da kudi ba ne, ko kuma ita Majalisar ta talauce, amma suna fuskantar matsin lamba daga jama’ar mazabunsu su yi musu abubuwa, wanda hakan ke taba kudadensu.

Dan Majalisar mai wakiltar Mazabar Darazo/Ganjuwa ta Jihar Bauchi, Mansur Manu Soro ya ce ikirarin da kakakin majalisar ya yi kan matsin lambar da suke fuskanta daga jama’ar da suke wakilta gaskiya ce.

“Kamar yadda ya ce, kasafinmu bai sauya ba a duk tsawon wadannan shekaru, duk da hauhawar farashin kaya. Yadda yake a lokacin da Dala take N200 har zuwa yanzu lokacin da take N400 bai saya ba.

“Ba cewa yake mun talauce ko kuma Majalisar kasa talautace ba. Yana nufin muna fuskantar matsi sosai na yi wa ’yan mazabunmu aiki a hannu daya, da kuma dukkan sauran ’yan Najeriya a daya bangaren.

“Kudaden da ake da su ba su isa su yi tasirin da ake bukata ba kuma kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na majalisa a wannan lokacin ba irin na baya ba ne. Abubuwa sun canza,” inji shi.

Wani babban dan majalisa da baya son a ambaci sunansa ya ce ba a tafiyar da kudaden majalisar yadda ya kamata.

“Rashin tsari ne. Ban da shugabannin Majalisar, babu wani daga cikinmu da zai iya gaya muku yadda ake gudanar da kasafin kudinmu,” inji shi.

Amma kakakin Majalisar Dattijai, Sanata Ajibola Basiru, ya yi watsi da bayanin rahoton da ke cewa Majalisar Tarayya ta dogara ne a kan ma’aikatun gwamnati, wajen samun kudaden gudanar da ayyukanta, yana mai cewa hakan zai iya haifar da rikici.

“Daga ma’aikata har ’yan majalisa babu wanda ke bin shugababbin Majalisar Tarayya bashin albashi. Kuma kuskure ne a ce majalisar za ta dogara da ma’aikatun gwamnati su dauki nauyin gudanar da ayyukanta.

“Muna da kasafinmu na kwamitocinmu da aikin sa ido; Idan kuma bukatu na musamman sun taso, kamar daukar kwararrun masu ba da shawara ko tafiye-tafiye na musamman don yin ayyukanmu, tsarin gudanawarwar Majalisa ke kula da su.

“Babu hikima a ce ma’aikatun da mu ke sanya ido a kan ayyukansu, da su muke dogara wajen samun kudade gudanar da ayyukanmu.

“Majalisar kasa tana daga cikin ayyukan sahun farko, saboda haka babu wani sanata ko dan Majalisar Wakilai da zai iya fitowa ya ce ba a biya shi ba,” inji shi.

Tsabar son kai ne –Masu fafutika

Wasu masu rajin kare hakkin jama’a sun ce kukan bukatar ‘yan majalisar ba ta dace ba kuma son kai ne.

Babban-Daraktan Cibiyar Bayar da Shawara da Wayar da Kai kan Sha’anin Majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya ce muddin Majalisar ta ki bayyana kasafin kudinta ga jama’a, to ’yan Najeriya ba za su gaskata da ikirarinsu na cewa ba ta da kudi.

“’Yan Najeriya na sane da irin rayuwar kasaitar da ‘yan majaliar suke yi. Me suke nufi da cewa Majalisar ba ta da kudade? Shin abubuwan su ne na kashin kansu ko kuma kudaden gudanar da harkokin majalisar?

“An sha kira a gare su da su bayyana wa jama’a kasafin kudinsu da yadda suke kashewa, amma sun ki yin hakan. Ya kuma kamata a bayyana tsarin sayayya na Majalisar ga jama’a daidai da dokar kasa.

“Hatta Odita-Janar na Kasa bai samu kyakkyawar amsa daga Majalisar ba game da kudaden da aka duba. Don haka ya kamata su zama masu nuna gaskiya a harkokinsu ta yadda ’yan Najeriya za su gaskata abin da suke fada,” inji Rafsanjani.

Shugaban Kungiyar Marubutan Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya (HURIWA), Kwamared Emmanuel Onwubiko, ya ce ikirarin da ’yan Majalisar cewa an ba ta da kudi yana nufin cewa an karkatar da kudaden da aka ba su.

Onwubiko ya ce “Bayanin na son kai ne, sakarci ne kuma ba shi da ma’ana.”

Shi ma Babban Daraktan, Cibiyar Bayar da Kare ’Yancin Dan Adam da Iliminntarwa (CHRICED), Dokta Ibrahim Zikirullahi, ya ce kafin a yi a yi la’akari da bukatar Majalisar ta karin kasafi, abin tambaya shi ne wane kimar amfani take kara wa dimokuradiyyar kasar.

Ya ce, “Tun daga kasafinta na 1999, shin Majalisar tana fayyace wa jama’ar Najeriya bayanan yadda take gudanar da kudaden?

“Shin sun yi rawar gani a matsayinsu na masu aikin ido don kawo kyakkyawan shugabanci a kasar?

“Idan har majalisar ta gaza a wadannan bagarorin, to kar ma ta taso da batun karancinn kudi.

“Gaskiyar magana ita ce Misali ta zama abin buga mummunan misali na yadda wani bangare na gwamnati zai iya zama bututun suke kudaden gwamnai.

“Idan ana maganar karin kudi don ta kara taka rawar gani, to wannan rainin hankalin ’yan kasa da suka dade cikin mawuyacin hali ne,” inji Zikirullahi.

 

Daga Sagir Kano Saleh Ismail Mudashir, Abdullateef Salau, Balarabe Alkassim daAbbas Jimoh