Dogayen layin ababen hawa sun ki daukewa a gidajen mai, duk kuwa da cikar wa’adin sa’a 48 da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ba wa dillalan mai na kawo karshen karancin man.
A ranar Litinin zuwa safiyar Talata an ci gaba da samun karancin mai da dogayen layi a gidajen mai a jihohin Kano, Kaduna, Kogi, Filato da kuma Yankin Birnin Tarayya a ranar Litinin.
- NAJERIYA A YAU: IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya?
- ’Yan fansho sun tarwatsa bikin rantsar da sabbin Ciyamomi a Neja
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Alhamis Shugaban DSS ya ba wa dillalan mai wa’adin sa’a 48 su kawo karshen karancin man, domin kawar da matsalar tsaro ko tarzoma a Najeriya.
Ya ba wa masu ruwa da tsakin wa’adin ne a wani zama da ya yi da jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) da kungiyoyin dillalan mai ta nsa (IPMAN) da manyan dillalan mai (MOMAN) da masu dafo-daf0 da kungiyar direbobi (PTD).
’Yar gidan jiya
Masu ruwa da tsakin sun kuma yi alkawarin kawo karshen matsalar, sai dai kuma har zuwa yanzu akwai cincirindon ababen hawa a gidajen mai a wasu manyan birananen Najeriya.
A yayin da matsalar ta ci gaba, ’yan bumburutu na cin karensu babu babbaka, suna sayar da litar man fetur a kan N350.
Wakilinmu ya ruwaito cewa gidajen mai da dama a Jihar Kano ba su yi aiki ba a ranar Litinin, ’yan kalilan da suka bude kuma sun rika sayarwa N280 zuwa N310.
Wani wanda ya sha man a Kano ya ce ya sayi lita a N310, saboda ba ya son bin dogon layi.
A garuruwan Kaduna da Jos kuma, yawancin manyan gidajen mai ba sa sayar ba.
Wani direban motar haya a Kaduna, Salisu Mohammed, ya ce: “Idan kana son mai sai dai ka je gidajen man bumburutu, da wuya manyan gidajen mai ke sayarwa, ko za su bayar sun fi ba wa ’yan bumburutu.”
A Lakwaja kuma an samu dogayen layin ababen hawa a gidajen mai, amma wasu da dama ba su sayar da man ba.
Wani wanda ya sha mai a Lakwaja, Yahaya Igono, ya ce ana sayar da lita a kan N210 zuwa N285.
Wani mazaunin garin ya ce, “Yanzu N1,800 ake sayar da lita hudu na fetur a wurin masu bumburutu.”
An samu sauki a Legas
Amma a Legas an dan samu sauki, inda wasu gidajen ke sayarwa N200 zuwa N220 kowace lita.
Manyan gidajen mai kamar Mobil na sayarwa N169/N170, amma kananan gidajen mai na sayarwa N230, N270 ko N320.
A kwaryar birnin Abuja ma an samu raguwar layika a gidajen mai, inda manyan gidajen mai ke bayarwa a N180, ko da yake matsalar ba ta kare ba a wajen gari, kamar unguwannin Kubwa da Lugbe.
A sakar mana mara —’Yan kasuwa
A nasu bangaren, dillalan sun ce samar da isasshen man da yanayin kasuwa da kuma sakar musu mara ne za su magance matsalar.
Shugaban Zauren Dillalan Mai na Arewa, Musa Yahaya Maikifi, ya ce dafo-dafon ’yan kasuwa na sayar da lita a N200, wanda shi ne silar samun karin farashin a Kano.
A cewarsa, wa’adin da DSS ta bayar abu ne da zai iya taimakawa wajen magance matsalar, amma “muddin ba a tace mai a kasar nan kuma NNPC zai ci gaba da amfani da Dala wajen shigo da tataccen, to da sauran rina a kaba.”
Shi kuma Shugaban Kungiyar Manyan Dillalan Mai ta Najeriya (MOMAN), Olumide Adeosun, shawara ya ba wa gwamnati ta tattauna da ’yan Najeriya ta yadda za a mayar da bangaren mai hannun ’yan kasuwa.
A cewarsa, “kasancewa gwamnati ta dade tana ba da tallafin mai, yanzu ba za ta iya magance matsalar mai da ake fama da ita ba.
“A halin yanzu duk wani bangare da aka samu tangarda a harkar samar da man, to sai ya haifar da dogayen a gidajen mai.”
Najeriya na da man kwana 30 a kasa –Rahoto
A ranar Lahadi Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Kasa (NMDPRA) ta sanar cewa Najeriya na da litar man fetur biliyan 1.879 a kasa, wanda zai isa kwana 30, tun da kasar na amfani da kimanin lita 60 a kullum.
Bincikenmu ya gano an kara yawan mai da aka sauke a dafo-dafo da ke fadin kasar daga na kwana bakwai zuwa na kwana 11.
Akwai kuma karin mai da zai kai kwana 19 da a halin yanzu ake kokarin saukewa a tashoshin jiragen ruwa.
DSS na binciken sirri
Hedikwatar DSS ta shaida mana cewa tana gudanar da binciken sirri, “tun tun daga ranar Alhamis, kuma duk wanda muka samu yana wa kasar nan zagon kasa zai yaba wa aya zaki.
“Shugaban Hukumarmu ya daura damarar sanya kafar wando da duk masu neman kawo barazanar tsaro a kasar nan,” in ji majiyarmu ta hukumar.
Ga koshi, ga kwanan yunwa
An shafe watanni ana fama da matsalar karancin mai a Najeriya, ga shi yanzu an shigo lokacin bukukuwan karshen shekara.
Dafo-dafo masu zaman kansu na sayar da lita a kan N180 sabanin N147 zuwa N150 da gwamnati ta kayyade.
A watan Yuli kamfanin NNPCL ta ce idan aka cire tallafi litar fetur za ta kai N462, domin a cewarta, tana biyan tallafin N297 a kan kowace lita, wanda shekara ya kai tiriliyan N6.5.
Sai dai kuma duk da tallafin, an shafe kusan rabin shekara wasu ’yan Najeriya ba sa iya samun man sai a hannun masu bumburutu kuma da tsada.
Daga: Sagir Kano Saleh, Simon E. Sunday & Idowu Isamotu (Abuja). Tijani Labaran (Lokoja), Ado Abubakar Musa (Jos), Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna), Zahraddeen Y. Shuaibu (Kano), Jide Olasunkanmi (Legas)