✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun ’yan kasuwa masu gauraya takin zamani da yashi ta cika a Jigawa

Suna hada yashi da takin NPK a buhu suna sayar wa jama'a yankin Hadeja.

Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Jigawa ta ce, ta cafke wasu mutum biyu dauke da takin zamani buhu 24 wanda aka yi ha’incin garwaya da yashi.

Mai magana da yawun hukumar, CSC Adamu Shehu ne ya ba da tabbacin kamun ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce an kama su biyun ne sun dura kasa cikin takin zamani samfurin NPK kafin daga bisani su kai su sayar wa jama’a.

Shehu ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata a Karamar Hukumar Hadejia.

Ya kara da cewa, laifin da suka aikata ya saba wa sassa na 184 da 97 na Dokokin Penal Code.

Ya ce tuni an gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu don fuskantar hukuncin laifin da suka aikata.