✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun matar da ta saci wayoyin iPhone guda 99 ta cika

An gurafanar da wata mata mai shekara 60 a kotun majistare da ke Ikejan jihar Legas, bisa zargin sace wayoyi kirar iPhone guda 99 da…

An gurafanar da wata mata mai shekara 60 a kotun majistare da ke Ikejan jihar Legas, bisa zargin sace wayoyi kirar iPhone guda 99 da suka kai kusan Naira miliyan 15.

Wacce ake zargin mai suna Adenike Okunbanjo, ’yar kasuwa ce da ke zaune a unguwar Temidire da ke karamar Hukumar Ibafo a jihar Ogun, kuma tana fuskantar tuhuma kan hadin baki da sata.

Dan Sanda mai gabatar da kara ASP Raji Akeem ya fadawa kotun cewa dattijuwar ta aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Janairun 2017, a filin jirgin Saman Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Akeem ya kuma ce wayoyin mallakin wani Mista Bolaji Ogunsanya ne, da ya aika da su Legas daga kasar Amurka  ga wani mai suna Mista Azeez.

Haka kuma Dan Sandan ya ce duk da wayoyin sun iso Legas din, amma sun bata a filin jirgin ko sam ko kasa, kuma duk kokarin gano su ya ci tura.

Akeem ya ce wanda ya shigar da karar ya baiwa ‘yan sanda lambar IMEI na dukkan wayoyin, kuma da su ne aka gano dattijuwar, har  aka kamo ta.

Kazalika ya ce binciken da ka yi a gidanta, ya kai ga gano hudu daga cikin wayoyin, laifin da ya ce  ya sabawa tanadin sashe na 287 da 411 na dokokin laifuka na jihar Legas, na shekarar 2015.

Sai dai wacce ake tuhumar ta musanta zargin, in da Alkalin kotun ya bada belinta kan Naira Miliyan biyu, da masu tsaya mata da suka mallaki makamantan su.

Za dai a cigaba da sauraren shari`ar ranar 28-Satumbar-2022.