Wadansu mutane da ake zargin sun kware wajen satar yara sun shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da ayarin ’yan sanda na musamman da ke yaki da masu garkuwa da mutane da ’yan kungiyar asiri suka yi musu kofar rago suka kama mutum 3 daga cikinsu.
A cewar mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar,DSP Abimbola Oyeyemi wadanda ake zargin sun kware wajen satar yara inda suka sace yara 8 a daidai lokacin da dubunsu ta cika. “Salon da suke amfani da shi shi ne, da zarar sun ga yaran da suke so su sata sai su tura mutum biyu a cikinsu mace da namiji wadanda za su shiga gidan yaran da zimmar neman gidan haya, ta haka suke amfani da dabaru su sace yaran,” inji shi.
Ya ce, “Lokacin da aka kama wadanda ake zargin wadanda suka hada da mata biyu masu suna Kate Njoku da Joy Okorie da namiji daya mai suna Onyeka Joseph an same su da wani yaro mai suna Temidayo Ajayi wanda suka sace a watan Yulin bara. Wadanda ake zargin sun shaida mana cewa, suna sayar da yaran ne ga masu bukata a Jihar Anambra, mun yi nasarar kama jagorarsu ce a Jihar Ondo bayan da rundunarmu da ke Ogun ta yi hadin gwiwa da takwararta a Ondo.”