Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) ta cafke wani mutum mai shekaru 28 bisa zargin yin garkuwa da wata karamar yarinya a Jihar Kwara.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar, Babawale Zaid Afolabi ya fitar ranar Talata a Ilorin, babban birnin Jihar.
- PSG za ta sayar da ’yan wasanta 10 saboda Messi
- Jama’a sun kona motar kwastam da ta kashe mutane a Jibiya
A cewar kakakin, wanda ake zargin ya hada baki da wasu mutane biyu da a yanzu ake nema ruwa a jallo wajen yin garkuwa da karamar yarinyar a kauyen Ilale da ke Karamar Hukumar Irepodun ta jihar.
Ya ce ababen zargin sun daure yarinyar a wani daji, inda suka yi mata fyade sannan suka tsere suka bar ta a nan.
“A ranar Alhamis, wani Yakubu Kelani ya zo ofishin NSCDC da ke Omu-Aran don bayar da rahoton cewa an sace ’yarsa mai shekara 15 a kan hanyarta ta debo ruwa a ranar 29 ga Yuli, 2021.
“An boye yarinyar a cikin wani daji inda rahotanni suka ce masu garkuwa da ita sun yi mata fyade kuma daga baya suka tuntubi danginta kan su biya Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa wanda iyayenta suka biya wani kaso daga ciki.
“’Yan banga sun damke daya daga cikin wadanda suka sace yarinyar a kasuwar Kara da ke Ajase lpo sannan suka mika shi ga jami’an NSCDC,” a cewar Afolabi.
Afolabi ya kara da cewa, yayin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya furta cewa ya aikata laifin tare da wasu mutum biyu da suka taimaka masa da a yanzu an bazama wajen neman su.
Ya ba da tabbacin cewa rundunar na bin sawun sauran wadanda ake zargi inda ya kara da cewa za a gurfanar da wanda aka cafke a gaban kotu bayan kammala bincike.