Dubun dubatar mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma masanin Hadisi, Dokta Ahmad Ibrahim-Bamba a birnin Kano.
An dai binne malamin, wanda ya rasu ranar Juma’a a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), a makabartar Dandolo.
Sheikh Bamba ya shahara da gudanar da Tafsirin Alkur’ani da Hadisai a Masallacin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) da kuma makarantarsa ta darul Hadith da ke unguwar Tudun Yola a cikin birnin Kano.
Marigayin, wanda ya rasu yana da shekara 82 a duniya, yana cikin malaman Musulunci masu fada a ji a ciki da wajen Kano.
Ranar Lahadi ne ya yi karatunsa na karshe, har ma ya sanar da hutu na dan wani lokaci, saboda yanayin jikinsa.
Dokta Bamba tsohon malami ne a Sashin Nazarin Harshen Larabci a Jami’ar Bayero da ke Kano, wanda ya ajiye aikin ya kuma dirfafi harkar da’awa da wa’azi gadan-gadan.
A shekarun baya, ana kiran malamin da sunan “Kala Haddasana”, wani lakani da masu halartar karatunsa musamman wanda ya shahara a kai na littafin Muwadda Malik suka sanya masa.
Bayanai sun ce dan asalin kasar Ghana ne kuma a can aka a haife shi.
A wata tattaunawa da wani dansa ya yi da manema labarai, ya ce mahaifinsa “ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir.
Bajimin malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.