✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS da EFCC na bincike kan tashin dala a kasuwar WAPA ta Kano

Za mu ci gaba da harkokinmu daga ƙarfe 12:00 na ranar Alhamis.

Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC sun soma bincike domin gano dalilin tashin gwaron zabi da dala ta yi a kasuwar musayar kuɗi a kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da kasuwar musayar kudade ta WAPA da ke Kano, ta ce ta rufe na wasu sa’o’i a yammacin ranar Laraba a daidai lokacin da farashin dala daya ya haura naira 1,500.

Kafar Watsa Labarai ta TRT dai ta rawaito cewa Sakataren Kasuwar Canjin Kudi ta WAPA a Kano Haruna Musa Halo ya ce sun rufe kasuwar ne sakamakon kiraye-kirayen da DSS da EFCC suke yi musu.

A cewarsa, hukumomin na ƙoƙarin jin bahasin da ya sanya dalar ke ci gaba da tashi kusan kullum, lamarin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.

Sai dai Sakataren ya ce a gobe Alhamis ne da karfe 12:00 na rana ne za su koma aiki da zarar lamura sun daidaita.

Ita ma dai Kungiyar ‘yan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya alakanta tashin gwaron zabi da dalar ta yi da ayyukan kamfanin hada-hadar kudade ta Intanet na Crypto da ake kira Binance.

Darajar takardar kudin Nairar dai ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru a tarihin Najeriya.