✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Drogba ya yi ban kwana da kulob din Galatasaray

Shahararren dan kwallon Kwaddebuwa Didier Drogba a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayar da sanarwar barin kulob din Galatasaray da ke Turkiyya bayan…

Didier DrogbaShahararren dan kwallon Kwaddebuwa Didier Drogba a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayar da sanarwar barin kulob din Galatasaray da ke Turkiyya bayan ya yi watanni 18 kacal yana wasa a kulob din.
A ranar 28 ga watan Janairun 2013 ne Drogba ya koma Turkiyya don cigaba da kwallo a kulob din.  Ya zuwa yanzu ya zura kwallaye 15 daga cikin wasanni 35 da ya yi wa kulob din.
 Drogba, wanda ya taba yi wa kulob din Chelsea na Ingila wasa ya yi amfani da kafar sadarwarsa ta Twitter ne wajen sanar da duniya halin da ake ciki inda ya gode wa magoya bayansa a kan irin hadin kai da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake wasa a kulob din.
Sai dai akwai yiwuwar dan kwallon ya canza sheka zuwa kulob din Jubentus da ke Italiya duk da zawarcin da kulob din Chelsea yake masa.
Tuni Mourinho ya nuna rashin gamsuwa da ’yan wasan gabansa Samuel Eto’o da kuma Fernando Torres don yake yake neman maye gurbinsu a kakar wasa mai zuwa

 

Yaya Toure… Yayin da Yaya Toure ya fara shirin rabuwa da kulob din Manchester City

Shahararren dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila kuma dan asalin Kwaddebuwa Yaya Toure ya nuna bacin ransa ga kulob din, ganin yadda ’yan wasa da mahukunta kulob din suka nuna masa halin ko-oho a bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Birthday) inda babu dan kwallon ko mahukunta kulob din da ya ziyarta sannan babu wanda ya aika masa sakon fatan alheri da hakan ya nuna ba shi da muhimmanci a gare su.
A ranar da City ta lashe gasar Premier ta Ingila ce dan kwallon ya cika shekara 31 kuma ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa, amma abin da ya daure masa kai shi ne babu wani dan kwallo ko  mahukunta kulob din da suka halarta sannan babu wanda ya aika masa sakon murna da fatan alheri.
Kamar yadda ejent din Toure mai suna Dimitry Seluk ya bayyana, wannan dalili ne ya sa dan kwallon ya fara shirin canza sheka zuwa wani kulob walau a ciki ko a wajen Ingila.
 Rahotanni sun nuna akwai yiwuwra dan kwallon ya koma tsohon kulob dinsa na da watau FC Barcelona da ke Sifen don cigaba da wasa a kakar wasa mai zuwa.