✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Donald Trump ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa

Ana zargin Trump da aikata laifuka 34, amma yaki amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.

Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, kuma dan takarar jam’iyyar Republican a zaben 2024, ya musanta aikata laifuka 34 da ake tuhumarsa da aikatawa.

Trump ya ki amsa laifinsa ne lokacin da ya bayyana a kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan a ranar Talata a birnin New York, kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.

Tsohon shugaban ya shafe kusan awa biyu a kotun ana gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Da yammacin Laraba ne ake sa ran zai koma Florida inda zai gabatar da jawabi a wajen taronsa na Mar-a-Lago, amma an tsare shi bayan halartar zaman kotun.

An gurfanar da shi a makon da ya gabata, Trump ya zama na farko a cikin tsoffin shugabannin Amurka da zai fuskanci tuhume-tuhume, kan shari’ar da ta shafi biyan kudi a 2016 ga tauraruwar fina-finan badala, Stormy Daniels.

A halin da ake ciki, sakataren yada labaran fadar White House a ranar Talata ta ki cewa komai kan tuhumar da ake yi wa Trump da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Karine Jean-Pierre ta ki amsa duk wata tambaya kan tuhumar da ake yi wa Trump a yayin taron manema labarai.

A cewar Jean-Pierre, Joe Biden ya mayar da hankali ga jama’ar Amurka ne, ba abin da ya shafi maganar wani daban ba.