✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Don yaki da kabilanci muka kafa kungiyarmu’

Yan kungiyar ’Yan Asalin Wasu Jihohi Mazauna Jihar Oyo (ANIRO) sun ce sun kafa kungiyarsu ne  domin yaki da kabilanci da wayar da kan jama’a…

Yan kungiyar ’Yan Asalin Wasu Jihohi Mazauna Jihar Oyo (ANIRO) sun ce sun kafa kungiyarsu ne  domin yaki da kabilanci da wayar da kan jama’a game da amfanin zama da juna da kuma lalubo hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Shugaban kungiyar Micheal Udeagha Orji, ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Wakilin Aminiya a Sakatariyar kungiyar da ke Birnin Ibadan a makon jiya.
Ya ce:  “Muna so a samu zaman lafiya a Najeriya, sannan  muna bukatar duk inda dan Najeriya yake ya dauki wannan wuri a matsayin mahaifarsa da zai gudanar da dukkan harkokin rayuwarsa ba tare da fargaba ba, sannan ya samu karbuwa a wurin jama’ar gari da mahukunta. Mun fito ne domin mu yi yaki da kabilanci, mu wayar da kan matasa don su yi watsi da batun dan kasa da bako a cikin garuruwa da jihohin kasar nan. Wannan yana daga cikin dalilan kafa wannan kungiyarmu ta (ANIRO)” inji shi.
Cif Micheal Orji, dan asalin karamar Hukumar Onu-Imo a Jihar Imo ne, ya yi kuruciya da karatu a garin Kakuri, Jihar Kaduna, yanzu kuma yake gudanar da harkokin kasuwancinsa a birnin Ibadan.
Makonni biyu da suka gabata masarautar Sasa ta nada shi sarautar dan Jikan Jihohin Yamma a dalilin kwazo da fafutukar lalubo hanyoyin zaman lafiya da kwato ’yancin jama’a da yake yi, ya ce “ban ga dalilin da zai sa mu rika kyamar juna ba, alhali muna aurar juna da harkokin kasuwanci tare.”
 Ya ce, “Na yi aure a nan Ibadan tare da haihuwar ’ya’yana duka a wannan gari, kuma dukkan harkokin kasuwancina a nan nake yi, sannan ba na nuna kabilanci wajen daukar ma’aikatan da suke aiki a karkashin kamfanonina, domin mafi yawanci daga Arewacin kasar nan suka fito, sannan akwai Yarabawa da yawa a cikinsu. Domin kyautata zamantakewa, na ki yarda in fifita ’yan asalin Jihar da na fito wajen daukarsu aiki a kan sauran jama’ar Najeriya. Irin haka kungiyar (ANIRO) take fatan ganin ana yi a ko’ina cikin kasar nan.”
Dangane da irin nasarori da kungiyar ta samu daga shekara 3 da kafuwarta sai ya ce, “kungiyarmu ta sha sasanta rikice-rikice tsakanin Fulani da manoma da tsakanin mahukunta da mutane musamman ’yan kasuwa wadanda ba ’yan asalin Jihar Oyo ba. Mafi yawancin kararrakin rikicin Fulani da manoma da ke gaban kotu kungiyar mu ce ta sasanta su, kuma mun karbo belin mutane da yawa da suke tsare a hannun ’yan sanda. Akwai wasu Hausawa ’yan kasuwa masu sayar da kayan marmari da gwamnati ta tashe su daga matsuguninsu a kasuwar Ogere da ke filin wasan kwallon Golf a Ibadan, kungiyarmu ce ta tashi tsaye wajen shiga tsakani da aka sasanta al’amarin. Sannan kungiyarmu tana da rassa masu yawa.”
Ya ce matsalolin da suke fuskanta shi ne ana yi wa kungiyar ANIRO kallon kungiyar siyasa da ke raba wa jama’a kudi, wanda hakan ya sa suka sha wahala wajen wayar da kan jama’a dalilin kirkiro kungiyar.